SiyasaAsiya
China ta yanke wa tsoffin ministocin tsaronta hukuncin kisa
May 7, 2026
Talla
Wata kotun soja a China, ta yanke wa tsoffin ministocin tsaron kasar biyu hukuncin kisa, sakamakon samunsu da aikata laifukan cin hanci da rashawa, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta Xinhua ta sanar.
Karin bayani:Firaministan Birtaniya zai kai ziyara Chaina
Tsoffin ministocin sun hada da Wei Fenghe da Li Shangfu, wadanda suka yi aiki tsakanin shekarar 2018 zuwa 2023, inda bayan shekaru biyu, za a mayar da hukuncin zuwa daurin ra-da-rai maimakon kisa, tare da kwace komai da suka mallaka a duniya.
Karin bayani:China ta gudanar da gagarumin atisaye a yankin Taiwan
Wannan dai wani bangare ne na yaki da cin hanci da rashawa da shugaban China Xi Jinping ya zafafa a kai, wanda ya gano mutanen da karbar na goro, a lokacin da suke rike da mukami.