Kasashen biyu na shirye shiryen tattaunawa a wannan makon
November 4, 2015Talla
Wannan tattaunawar dai na kasancewa irin ta farko tun lokacin da bangarorin suka dare biyu bayan yakin basasar kasashen a shekara ta 1949.
Ana saran cewar tattaunawar zata bada wata kafar kara kyautata dangantaka a tsakanin bangarorin biyu tare da samun dai -dai tuwa a tsakanin su.
Kazalika Amirka a nata bangaren na maraba da wannan matakin kana kuma za ta sanya idanu sosai akan tattaunawar da zata gudana a tsakanin Chinan da Taiwan ata cewar fadar White House ta Amirka.