1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta soke hukumcin kisa

April 29, 2020

Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da soke hukuncin kisa a jerin hukunce-hukuncen da dokar yaki da ta'addanci ta kasar ta tanada, bayan bukatar haka da gwamnati ta yi. 

https://p.dw.com/p/3bZ65
Proteste gegen Freilassung von Asia Bibi in Pakistan
Hoto: AFP/Getty Images/A. Hassan

Baki dayan 'yan majalisar dokokin kasar ne dai suka amince da matakin kwaskware dokar wanda gwamnatin kasar ce ta gabatar da bukatar a gaban majalisar a watanni shida da suka gabata.

A nan gaba ne dai Shugaba Idriss Deby, wanda ke da rinjaye a majalisar dokokin zai rattaba hannu kan dokar a hakumance. 

A shekara ta 2016 kasar ta Chadi ta soke hukuncin kisa, ban da wadanda aka samu da laifin ta'addanci.

A cewar kasar ta dauki matakin yi wa dokar gyaran fuska ne ta yadda za ta dace da ta sauran sauran kasashen nan na G5 Sahel wadanda suka soke hukuncin na kisa har ma ga wadanda aka samu da laifin ta'addanci.