1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta samu sabon Firamnista

October 12, 2022

Sa'o'i bayan sanar da murabus din tsohon firaminista a Chadi, an bayyana sunan wani sanannen dan bangaren hamayyar kasa a matsayin sabon firaminista a kasar.

https://p.dw.com/p/4I6Sj
Janar Mahamat Idris Deby tare da Firaminista Saleh Kebzabo
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft der Republik Tschad

An bayyana fitaccen 'yan siyasar nan na bangaren hamayya a Chadi, Saleh Kebzabo a matsayin sabon firaministan kasar.

An sanar sunan Kebzabon ne kwana guda da murabus din tsohon firaministan kasar, Pahimi Alber.

A karshen makon jiya ne dai taron kasa ya amince da wa'adin watanni 24 a matsayin lokaci da kasar za ta yi zabe zaben da zai maida ta ga mulkin farar hula.

An kuma amince Janar Mahamat Idriss Deby Itno, a matsayin shugaba na riko da aka ce yana iya tsayawa takara azaben kasar.

Cikin watan Afrilun bara ne kuwa Janar Mahamat Idris Debyn mai shekaru 38 ya kama mulki bayan mutuwar mahaifinin Idris Deby wanda ya yi mulkin shekaru 30.

Tun da fari dai Janar Mahamat Idris Deby, ya yi alkawarin ba zai nemi wata takara a Chadin ba.