Chadi na rawar gani a yakar Boko Haram | Siyasa | DW | 04.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Chadi na rawar gani a yakar Boko Haram

Kasar Chadi ta samu wata dama ta kasancewa mai taka rawar gani a fannin tsaro a kasashen Afirka, ta Yamma da ma ta Tsakiya, ganin yadda kasar ta amsa kiran kamaru wajan yaki da Boko Haram.

Tschad Präsident Idriss Deby 3.4.2014

Shugaba Idriss Deby na kasar Chadi

A firar da DW ta yi da shi, Lucien Pambou wani malamin Jami'a a kasar Faransa daya daga cikin masharhanta kan siyasar Afirka, ya dubi matakin na kasar Chadi a matsayin wani abu da zai kara mata kwarjini.

Duk da cewa Shugaban kasar Chadi Idriss Deby na daya daga cikin shugabannin da ake nunawa da dan yatsa a fannin matsalar kiyaye hakkokin bil-Adama a cikin kasashensu, ganin kuma yadda yake da masu adawa sosai a cikin kasarsa gami da manufofinsa na mulki, ana iya cewa tsunduma da wannan kasa tayi cikin yaki da kungiyar Boko Haram na a matsayin wani mataki da ke kokarin canza iri-irin kallon da a da ake yi wa magabatan kasar ta Chadi. Sai dai a cewa Farfesa Lucien Pambou malamin Jami'a a kasar Faransa kuma masanin Siyasar Afirka, shigar kasar Chadi cikin yaki da kungiyar ta Boko Haram na da dalillai biyu:

" Dalili na farko dai shi ne na ganin wannan kungiya ta Boko Haram tana da wani buri na kafa nata Khalifa wanda zai shafi kasashen na Najeriya, Kamarun Nijar da kuma Chadi, sannan wani dalili na biyu shi ne ganin yadda kasar Chadi take a matsayin cibiyar dakarun kasar Faransa masu yaki da ta'addanci a yankin Sahel, na nunin cewa kasar Chadi tana da babban mahimmanci a fannin yaki da ta'addanci a yankin Sahel da Sahara, da kuma yankin Afirka ta Tsakiya."

Tuni dai wasu ke ganin cewa wannan wata dama ce ga shugaba Deby ta dawo da martabarsa a idanun makwabtansa, da ma kasashen duniya, tun bayan da ya amsa kiran shugaban kasar Kamarun na bada tallafi wajan yaki da kungiyar Boko Haram wanda kawo yanzu ake ci gaba da ganin haske tare da nasara ga dakarun kasar ta Chadi a cikin yakin da suke da Boko Haram kamar yadda Farfesa Lucien Pambou ya yi tsokaci a kai:

" Lalle a cikin kasarsa Shugaba Deby mutun ne da ke fuskantar adawa sosai daga al'ummarsa, amma kuma tun bayan da ya amince da taimaka wa makwabciyarsa kasar kamarun kan yaki da Boko Haram, hakan na baiwa Shugaban na Chadi wata dama ta wanke kai daga zargi, inda farin jininsa ke dada karuwa."

To ko wane mataki ne ta kamata kasashe makwabtan kasar ta Chadi da ma sauran kasashen Afirka su dauka dangane da yadda suke kallon kasar Chadi, zasu tsaya ne suna zargin hukumominta da wasu laifuka, alhali kuma kungiyar Tarayyar Afirka na shirin girka wata runduna wadda zata kumshi dakaru dubu bakwai da dari biyar wadda kuma ake ganin cikinta kasar ta Chadi za ta taka rawar gani anan ma Farfesa Lucien Pambou ya ci gaba da cewa:

" Lalle ne ya kyautu wannan aniya da kasar Chadi ta dauka na yakar 'yan kungiyar ta Boko Haram ta kasance cikin nazari na gaba daya, wanda a cikinsa ala tilas shugabannin kasashen Afirka zasu tashi ne ba tare da wani bata lokaci ba ta hanyar bada kayayyakin aiki da duk abubuwan da suka kamata wajan horo da samar da dabaru ga dakarunsu"

Sauti da bidiyo akan labarin