Chadi: Boko Haram na samun hadin bakin jama′a | Labarai | DW | 04.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi: Boko Haram na samun hadin bakin jama'a

Hukumomi a kasar Chadi sun koka da yadda al'ummomin yakunan tafkin Chadi ke bayyna wa mayakan Boko Haram wasu bayyanan sirri da ke ba su damar kai farmaki ga jami'an tsaro da sauran ayyukan ta'addanci.

Kasar Chadi ta zargi kungiyar Boko Haram mai gwagwarmaya da makamai a yankin Tafkin Chadi da samun hadin bakin al'ummar da ke kauyukan da mayakan na jihadi ke kai farmaki.

Shugaban Kasar Chadi Idriss Deby Itno ne ya bayyana wannan zargin a wannan Talatar, yana mai cewar kamata yayi a tona asirin duk wani wanda ake zargin yana hada baki da kungiyar wajen bata asirin lunguna da sakunan da za ta iya kai farmaki ga jami'an tsaro.

Shugaban ya ce idan har yan ta'addan Boko Haram za su iya shiga har a jerin sojojin kasashen su kuma aikata harin ta'addanci, to ba shakka hakan na tabbatar da cewa suna samun hadin bakin wasu jama'a da ke yankunan da mayakan ke kai hare-haren.

Shugaban na jawabin ne a daidai lokacin da wasu sojojin kasar hudu tare da dan jarida guda suka kwanta dama sakamakon taka nakiyar da motarsu ta yi a yayin wani sintiri a yammacin kasar Chadi.
 

  • Kwanan wata 04.06.2019
  • Mawallafi Abdoulaye Mamane Amadou