1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cece-kuce kan taron kasa a Tarayyar Najeriya

October 2, 2013

kungiyoyin kare hakkin jama’a da masharhantan Najeriya na mayar da martani a kan tasirin da kwamitin gudanar da taron sulhuntawa a tsakanin ‘yan Najeriya zai yi a daidai lokacin da ake fuskantar kalubalen tsaro..

https://p.dw.com/p/19t0b
Nigeria Abuja MilitärparadeHoto: DW/U. Musa

Kodayake shugaban Najeriyar ya yiwa taron lakabi da na sulhuntawa a tsakamin 'yan Najeriya, amma dai masharhanta da ma masu fafutukar kare hakin jama'a sun bayyana shi da taron kasa na sanin makomar Najeriyar domin a samo mafita daga dimbin matsalolin da suka addabi Najeriyar a tarihinta na kasancewa a hade a shekaru 53. To ko ya kungiyoyin kare hakin jama'a ke kalon wannan aniyar ta shugaban Najeriyar? Hajiya Saudat Mahdi it ace sakatariyar gudanarwa kungiyar kare hakkokin mata ta Wrapa da ke Abuja, ta ce "an matsalolin da ke damun Najeriya da kuma hanyoyin da za a bi wajen samun sauki."

Kokuwar kame madafan iko da ma wasoson dukiyar da Najeriyar ta malaka da tuni aka yi nisa da tsarin gafiya ta tsira da na bakinta ya sanya kabilun Najeriya yi wa juna kalon hadarin kaji har ma da furta kamalami masu nauyi a game da makomar kasar da shugaban ke hangen taron irin wannan zai iya sulhuntawa. To sai sanin cewa ba wannan ne farkon shirya tarurrunka makamantan irin wannan ba, ya sanya Malam Abubakar Umar Kari jefa shakku a kan tasirin da sakamakonsa ka iya yi, inda ya ce shugaban kasa" ya kamata ya sansanta da mutanen Najeriya, saboda a 'yan watannin nan abubuwa sun sha farauwa, wadanda za a iya cewa mukarrabansa ne ke furta kalaman da ke kara raba kan al'uman Najeriya."

Nigeria Proteste gegen Kinderehe
Zanga-zanga da yajin aiki na neman zama ruwan dare a NajeriyaHoto: picture alliance/AP Photo

.Masu goyon bayan wannan shiri na kallonshi a matsayin gagarumar kyauta da shugaban Najeriyar ya yiwa al'ummar kasar a bikin cika shekaru 53 da kafuwa. Sai dai tuni wasu yan kasar irinsu Saidu Umar Kumo mai taimakawa shugaban jam'iyyar PDP na kasar bayyana cewa bai ga abin jin tsoro ga lamarin ba. kungiyoyi irin na 'yan kabilar Yarbawa zalla ta Afenifire da ma ta tuntubar juna a arewacin Najeriya sun yi marhabin da shirya shin. Sannan ana shirin gudanar da shi ne a daidai lokacin da Najeriyar ke jajibarin cika shekaru 100 da haihuwarta a yanayi da ke cike da kalubale ga tarihin kasar.

House of Representatives in Nigeria
Majalisar Najeriya ma na tafka muhawara akan taron kasaHoto: CC BY-SA 2.0

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe