1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

CDU ta tsayar da wanda zai gaji Angela Merkel

April 12, 2021

Mambobin jam'iyyar CDU a Jamus sun mara wa Armin Laschet da suka ce zai gaji Angela Merkel bayan karewar wa'adinta nan gaba a bana, duk da cewa an samu wani igo da ya tsaya.

https://p.dw.com/p/3rt2U
Deutschland | Armin Laschet | Ministerpräsident NRW
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Jam'iyyar CDU ta Shugabar gwamnatin Jamus, ta goyi bayan aniyar shugabanta Armin Laschet ta neman kujerar shugabancin gwamnati a zaben kasa da za a yi cikin watan Satumba.

Sakataren jami'iyyar, Paul Ziemiak, ya ce Laschet ya sami goyon bayan mambobin jam'iyyar, da ma na wasu daga cikin 'yar uwar tagwaitakar CDU wato jam'iyyar CSU duk da cewa shugaban CSU Markus Soeder na neman matsayin shugabancin gwamnatin, mutumin da ya ce bai janye aniyarsa ba.

Sakataren jam'iyyar CDU Ziemiak, ya bayyana goyon bayan da Laschet ya samun ne dazu-dazun nan a lokacin wani taron manema labaru bayan matsayar da aka cimma a yau Litinin.