CAN ta yi kiran kawo karshen rikicin jihar Filato | Zamantakewa | DW | 20.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

CAN ta yi kiran kawo karshen rikicin jihar Filato

Kungiyar Kristoci a Najeriya ta yi kira ga duk bangarorin da ke rikici da juna a jihar Filato tare da gwamnati da ta kara kaimi a kokarinta na sassanta bangarorin da ke rikici da juna don samun maslaha a jahar.

Kiran ya biyo bayan sabon rikicin da ya kunno kai a tsakanin wasu kabilun jihar Filato da Fulani makiyaya lamarin da ya dauki hankalin kungiyar Kristocin Najeriya da ta nemi daukar mataki na ba sani ba sabo akan duk wanda aka samu da laifi a wani mataki na shawo kan rikicin da ke barazana ga zaman lafiyar al'umma, hakan zai zama mafita inji kungiyar. Abin da ya fi daga hankali a rikicin baya bayan nan shi ne yadda rayuka suka salwanta duk da dokar hana fitar dare da aka sanya, lamarin da aka danganta da siyasa. Pastor Daniel David Kadzai shi ne shugaban kungiyar Kristocin Najeriya a bangaren matasa, ya kuma yi wa matasa nasiha kan rungumar tsari na zaman lafiya kamar yadda ya shedawa manema labarai a abinda ya kira kokarinsu na samar da zaman lafiya a jahar.

Kungiyar Kristoci bangaren matasan na mai bayyana rashin gamsuwa a kan rashin daukan matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar, musamman kamawa da hukunta masu laifi sai dai ministan matasa da wasani na Najeriya Barrista Solomon Dalung ya ce akwai matakin da suka  dauka musanman na damawa da matasa. Ana fatan cewa tarba-tarbar da ake yi wa rikicin na jihar Filato zai yi tasiri a matakin da ake dauka don murkushe duk wata sabuwar fitina, Mutane da dama sun halaka a ‘yan shekarun bayan nan a tashe tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini a jihar ta Filato duk da cewa a baya an sha cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu dake rikici da juna.

 

Sauti da bidiyo akan labarin