Bush ya sanya hannu kan dokar kara matsawa gwamnatin Sudan lamba | Labarai | DW | 31.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bush ya sanya hannu kan dokar kara matsawa gwamnatin Sudan lamba

Shugaba Bush na Amurka ya sanya hannu kan wata doka da ta amince da ƙara matsawa gwamnatin Sudan lamba a fannin tattalin arziki sakamakon abinda ke faruwa a lardin Darfur. Bush yace gwamnatinsa zata ci gaba a ƙoƙarin da take yi na ganin an samu ci gaba mai ma’ana a lardin Darfur ta hanyar kafa takunkumi kan gwamnatin Sudan da kuma a fannin diplomasiya tare da bada goyon baya ga aikewa da dakarun wanzar da zaman lafiya a Darfur. Dokar dai tana mai bada shawara ne ga hukumomin Amurka da kuma masu saka jari masu zaman kansu da janye daga saka jari a kanfanoni dake hulɗa da Sudan.