Burundi: ′Yan majalisa sun soki kamun ′yan adawa | Labarai | DW | 18.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burundi: 'Yan majalisa sun soki kamun 'yan adawa

Wani gungun 'yan majalisar dokokin kasar Burundi ya fitar da sanarwa inda ya soki matakin kame-kamen da hukumomin kasar ke yi wa masu fafutikar yaki da sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Uganda Burundi-Friedensgespräche in Entebbe (picture-alliance/AP Photo/S. Wandera)

'Yan adawar kasar Burundi

Hukumomin na kasar Burundi dai sun kira zaben raba gardama kan batun kwaskware kundin tsarin mulkin kasar a watan Mayu mai zuwa, wanda kuma idan aka amince da shi, hakan zai bai wa shugaban kasar Pierre Nkurunziza da ke mulkin kasar tun daga shekara ta 2005 damar sake tsayawa takara a shekara ta 2020, inda zai iya sake neman wani wa'adin mulki har sau biyu na tsawon shekaru bakwai-bakwai.

Tun dai daga ranar 12 ga watan Disamba da ya gabata ne gwamnatin ta Burundi ta ayyana wani rangadi na fadarkar da 'yan kasar kan sauye-sauyen da take shirin yi, abun da suma masu adawa da shirin suka shiga ta su fadarkarwar. Sai dai kuma gwamnatin na zargin masu adawa da tsarin da yin yakin neman zabe tun kafin lokaci inda ta kame sama da 40 daga cikinsu.