Burundi: 'Yan gudun hijira cikin wahala | Zamantakewa | DW | 16.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Burundi: 'Yan gudun hijira cikin wahala

'Yan Burundi sama dubu 70 ne rayuwarsu ke ci gaba da tagayyara, a sansanonin 'yan gudun hijira a Ruwanda tsawon shekaru biyar da suka gabata, abin da suka dora alhakinsa kan tsohon shugabansu marigayi Pierre Nkurunziza.

Ruanda Flüchtlinge aus Burundi

'Yan gudun hijirar Burundi na cikin halin tasku a Burundi

Ga 'yan gudun hijirar dai, tsawon shekaru biyar da suka gabata zasu iya tuna mulkin shugaba Pierre Nkurunziza ne kawai da kashe-kashe da jefa mutane a gidajen kurkuku da tilastawa wadanda ke adawa da shi tafiya gudun hijira.

Da me za a tuna Nkurunziza?

Da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar dai za su tuna marigayi Nkurunziza da a lokacin da ya rasu ke da shekaru 55 a duniya ne kawai da rigingimu da suka mamaye wa'adin mulkinsa na uku. Tun bayan sanar da mutuwarsa a makon da ya gabata ne dai, 'yan gudun hijirar suka fara yin martani mabanbanta dangane da yiwuwar komawa gida domin sake farfado da rayuwarsu. A shekara ta 2015 nedai Burundi ta fada cikin rigingimun siyasa, sakamakon yadda Nkurunziza ya sa kafa ya shure kundin tsarin mulkin kasar domin neman wa'adin mulki a karo na uku bayan yunkurin kifar da gwamnatinsa ya ci tura.

Burundi Pierre Nkurunziza 2005

Marigayi Pierre Nkurunziza na Burundi

Ga mafi yawa daga cikin 'yan gudun hijirar Brundi da ke Ruwanda dai, Nkurunziza zai kasance cikin tarihi, a matsayin tsohon shugaban kasa mai kwadayin mulki a hanyar rike madafun iko ko ta wane hali, sai dai kuma ya mutu kafin ya karasa wa'adin mulkinsa na uku da ya yi fafutukar samu.

Mutuwa ba tare da girbarbe shuka ba?

Duk da cewa yawancin 'yan gudun hijirar Burundi da ke Ruwanda, na dokin komowa gida bayan mutuwar Nkurunziza sun nuna bakin cikin mutuwarsa ba tare da gurfana a gaban kuliya domin amsa miyagun laifukansa ba. Ba da jimawa ba ne dai Kotun Hukunta ma su Aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ICC, ta sanar da cewar tun a shekara ta 2017 ta kaddamar da bincike tare da gabatar da sakamakonsa kan miyagun shugabannin Burundi, kuma Nkurunziza na cikinsu.

Pierre Nkurunziza dai ya taso maraya,  bayan mutuwar iyayensa a rikicin kabilanci na 1972. Yawancin al'ummar Burundi sun yi zaton zai sauya tarihin kasar, ta hanyar hada kan al'ummarsa da watsi da da kabilanci. Sai kuma an samu akasin haka. Duk da wadannan munanan zargi, shugabanin kasashen yankin kamar Uhuru Kenyatta na Kenya, sun yi bakin cikin mutuwarsa tare da bayyana shi a matsayin jarumin da ya jajirce wajen daidaita kasarsa.