Burundi ta fice daga cikin kotun duniya | Labarai | DW | 19.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Burundi ta fice daga cikin kotun duniya

Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi ya saka hannu kan ayar dokar tsame kasar daga cikin kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki.

Shugaba Pierre Nkurunziza na kasar Burundi ya saka hannu kan ayar dokar da ta fitar da kasar daga cikin kotun duniya mai hukunta manyan laifuka, bayan a makon jiya majalisar dokokin kasar da gagarumin rinjaye ta kada kuri'ar fita daga kotun.

Burundi wadda ta fada cikin rundanin siyasa tun shekarar da ta gabata ta 2015 lokacin da shugaban ya dauki matakin neman wa'adi na uku na mulki. Kuma gwamnatin kasar ta harzika sakamakon matakin Majalisar Dinkin Duniya na neman bincike kan kisan kimanin mutane 450 sannan wasu dubban suka tsere, wanda ake ganin zai kai ga cafke wasu gaggan gwamnatin kasar ta Burundi. Kasashen Afirka da dama sun nuna rashin jin dadi kan yadda kotun ta duniya take nuna musu tsangwama.