Burundi da Corona a Afirka a jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 19.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Burundi da Corona a Afirka a jaridun Jamus

Sabon shugaban kasar Burundi ya karbi jan ragamar kasa mai fama da rikici inji jaridar Süddeutsche Zeitung yayin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce yakin da ake yi da annobar corona ya janyo karin matsaloli.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta buga labari kan annobar cutar Corona a nahiyar ta Afirka tana mai cewa yakin da ake yi da annobar ya janyo karin matsaloli a wasu lokutan ma fiye da annobar kanta. Jaridar ta fara da ba da misali da kasar Afirka ta Kudu inda a biranen kasar da dama musamman a unguwannin talakawa ake ganin dandazon jama’a fiye da kima da zarar masu ba da tallafin kayan abinci sun isa wuraren. Kusan watanni uku da sanya dokar kulle kasar na dab da rugujewa, wasu masharhanta ma na cewa kasar ta zama mai karbar tallafi, wasu kungiyoyin agaji sun ce suna kara fama da karancin kayan agajin da za su ba wa mabukata.Yawan marasa aikin yi a kasar ya karu da kusan kashi 50 cikin 100, sakamakon cutar Corona.

Südsudan Juba Corona-Krise (Getty Images/AFP/A. McBride)

Kasashen Afirka na ci gaba da daukan matakai don yakar corona

Duk kanwar ja ce a sauran kasashen Afirka da yanzu haka ke fama da matsaloli sakamakon karayar tattalin arzikin duniya. Rufe iyakokin kasashe ya sa ba a iya jigilar kayan abinci yadda ya kamata daga wata kasa zuwa wata. Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadi na yiwuwar fuskantar matsananciyar 'yunwa a Afirka da za ta yi sanadin rayukan mutum kimanin miliyan 65 kafin karshen wanna shekara. Rufe iyakokin kuma ya kawo cikas ga yakin da ake yi da zazzabin cizon sauro saboda rashin isar gidan sauro a wuraren da ake bukata, saboda haka ake hasashen yawan wadanda za su mutu a dalilin cutar maleriya zai ninka sau biyu a bana.


Corona ta hana shugabanni halartar bikin rantsar da sabon shugaban Burundi

Sabon shugaban kasar Burundi ya karbi jan ragamar kasa mai fama da rikici inji jaridar Süddeutsche Zeitung, sannan sai ta kara da cewa a ranar Alhamis aka yi bikin rantsar da Évariste Ndayishimiye a matsayin sabon shugaban kasar Burundi bayan mutuwar ba-zata ta Shugaba Pierre Nkurunziza da ya shugabanci kasar tsawon shekara 15. Sai dai bikin bai samu halarcin shugabanni daga wasu kasashen ba saboda rufe iyakokin kasashe sakamakon cutar corona. 

Burundi Vereidigung Präsident Evariste Ndayishimiye (Getty Images/AFP/T. Nitanga)

Evariste Ndayishimiye na da jan aiki wajen hade kan 'yan Burundi

Jaridar ta ce Nkurunziza dai ya yi mulki irin na kama karya, shi ya sa ta ce ta yi mamaki da magajinsa ya yi alkawarin ci gaba da bin tafarkinsa wajen yin abin da ya kira aiki na gari. Ko da yake zai yi wahala a yi hasashen alkiblar sabon shugaban amma jaridar ta yi fatan zai jawo 'yan adawa a cikin tafiyar sama wa kasar mafita daga matsalolin talauci, karaya tattalin arziki da cin hanci da rashawa da tashe-tashen hankula.


Rawar da Jamus ta taka a wariyar launin fata a Namibiya

An ga alamun cimma matsaya a takaddamar da ake yi na hannun Jamus a kisan kare dangi a Namibiya a zamanin mulkin mallaka, wannan shi ne taken labarin da jaridar Der Tagesspiegel ta buga, inda ta fara da tabo zanga-zangar adawa da wariyar launin fata a Amirka da kasashen Turai, inda masu fafatuka ke lalata mutum mutumin tsoffin jagororin Turawan mulkin mallaka da ake zargi da taka muguwar rawa a zamanin mulkin mallaka a Afirka.

Namibia Unabhängigkeitskampf 1989 (picture-alliance/AP Photo/B. Paddock)

Wariyar launin fata a Namibiya ya zame wa Jamus kashin kifi a wuya

 Wannan ya sa jama’a ta sake yin tuni da tarihin ta’asar da Jamus ta aikata a lokacin mulkin mallaka a Afirka, musamman ma kisan kare dangi da ta yi wa ‘yan kabilun Herero da Nama a yankin da yanzu ya zama kasar Namibiya. Kimanin mutane maza da mata manyan da yara dubu 80 ne wannan ta’asar ta shafa. Yanzu an dukufa don ganin an bude sabon babi da zai samu karbuwa ga bangarorin biyu wato Jamus da al’umomin na kasar Namibiya. Bayan shekaru biyar na tattaunawa an dab da cimma matsaya bayan neman afuwa a hukumance da Jamus ta yi.

Sauti da bidiyo akan labarin