Burkina Faso: AU na neman mafita a rikicin siyasa | Siyasa | DW | 10.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Burkina Faso: AU na neman mafita a rikicin siyasa

Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Mohamed Ould Abdel Aziz ya gana da sabon shugaban gwamnatin mulkin soji na Burkina Faso Lt-Kanar Isaac Zida a Wagadugu.

Shugabannin biyu sun gana a birnin Wagadugu fadar gwamnatin kasar ta Burkina Faso. Shugaban Mauritaniya da yake rike da shugabancin Tarayyar Afirka Mohamed Ould Abdel Aziz ya shaida wa manema labarai cewa an yi ganawar domin samar da mafita bisa rikicin siyasar kasar ta Burkina Faso. Ya bayyana haka bayan ganawa da shugaban gwamnatin mulkin soji Lt. Kanar Isaac Zida. Sannan ya ce ziyarar bata da nasaba da saka takunkumi.

Kasar ta Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka ta fada cikin rudanin siyasa a watan da ya gabata. lokacin da Shugaba Blaise Compaore ya yi yunkurin sauya kundin tsarin mulkin domin tsawaita mulkinsa na tsawon shekaru 27.

Mauretanien Mohamed Ould Abdel Aziz Präsident

Shugaban Kungiyar AU Mohamed Ould Abdel Aziz

Wannan lamari ya fusata 'yan kasar wadanda suka gudanar da zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin Compoare.

Wani kiyasi ya nuna fiye da mutane 180 suka jikkata sakamakon zanga-zangar a birnin Wagadugu. Augustin Loada farfesa kan harkokin siyasa ya nunar da cewa samun mutane masu kima shi ne abin da ya dace wajen kafa gwamnatin wucin gadi:

"Anan batun shi ne na samun mutumin da kowa ya amince da shi wanda zai jagoranci rikon kwaryar wannan kasa ta Burkina Faso. Kun san duk lokacin da ya yi yana mulkin wannan kasa Blaise Compaore bai samu nasarar hada kan 'yan kasar ba ta hanyar sanya yarda a tsakani kuma haka shi ne ke kawo matsaloli yanzu"

Kasar ta Burkina Faso mai mutane kimanin miliyan 16 za su ci gaba da zaman jira yadda za a wanye kan samar wa kasar da manufa ta gaba kan rike madafun iko.

Sauti da bidiyo akan labarin