1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: An kashe mutane 170 cikin mako guda

March 3, 2024

Hukumomi a Burkina Faso sun ce, kimanin mutane 170 ne aka kashe a kauyuka uku da ke arewacin kasar a cikin mako guda.

https://p.dw.com/p/4d7Dl
An kashe mutane 170 a kauyaka guda uku na arewacin Burkina Faso
An kashe mutane 170 a kauyaka guda uku na arewacin Burkina FasoHoto: Sebastien Rieussec/Hans Lucas/IMAGO

Dan sanda mai gabatar da kara na Burkina Faso, Aly Benjamin Coulibaly ya ce, sun samu rahotannin kai hare-hare a kauyukan da ke lardin Yatenga a ranar 25 ga watan Fabarairun da ya gabata.

Kazalika an kai wasu mabambantan hare-hare a wani masallaci da kuma mujami'a da ke arewacin kasar.

Tuni dai aka kaddamar da bincike kan harin da ya raunata gomman mutane da kuma lalata dukiyoyi. Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Kasar Burkina Faso ta sha fama da rikcin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai da suke da alaka da Al-Qaeda da kuma IS.