Bukola Saraki ya ce ba shi da laifi | Siyasa | DW | 22.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bukola Saraki ya ce ba shi da laifi

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya musanta laifuffuka 13 da ake zarginsa da aikatawa, a kotun da’ar ma’iakata.

Bayyanarsa a kotun dai ya kawo karshen kuli kuciyar da aka dade ana yi a tsakanin sanata Saraki da kotun, wanda duk da kokarin da ya yi na kaucewa bayyana ya ci tura a kotuna uku da ya nufa. An dai kai ruwa rana kafin fara shari'ar inda lauyan da ke kare Bukola Sarakin ya dage kan ba zai shiga kejin wadanda ake zargi ke zama. Barrister Rotimi Jacob ya bayyana yadda suka shari'ar ta kasance.

‘'Wannan ci gaba ne, kas an irin matsalolin da muka fusknata sun zo da nasu dubaraun sun tabbatar da cewa bai amsa yana da laifi ko a'a ba, amma mun samu shawo kan wannan matsala, a karshe ya yi hakan yanzu zamu fara aikihin shari'ar''.

Kotun ta bayar da belin Saraki

An dai dauki tsauraran matakai a kotun inda shiga ciki ya zama babbar matsala. To ko yaya bangaren Sanata Bukola suka ji da sakamakon shari'ar? Barrister Joseph Daudu shi ne lauyan da ke kare Sanata Bukola Saraki.

‘'Mun dai kai inda ake so mu tsaya watau shiga akwatin wanda ake zargi, aka karanta laifuffuka da wani jawani da y yi man day a faranta man rai cewa yanzu ne ya fara jin wannan tuhumar da aek mashi. Mu dai zamu ci gaba da kare shi yadda muka saba, don haka muna jiran ranar 21 zuwa 23 ga wata mai zuwa''.

An bada belin Sanata Saraki bisa matsayinsa nakashin kansa, tare da dage sauraren shari'ar har zuwa ranar 21 zuwa 23 ga watan nan domin ci gaba da saurane shari'ar. Wannan dai tuhuma ce da kedaukan hankali domin shine karon farko da mutum na uku a matsayin Najeriya ke fusknata tuhuma wanda ba kasafai ake samun irin haka ba a baya.

Sauti da bidiyo akan labarin