Bukatar dena dogara da Amirka kan tsaro | Labarai | DW | 27.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bukatar dena dogara da Amirka kan tsaro

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana a ranar Litinin cewa zai gabatar wa Kungiyar Tarayyar Turai bukatar kara inganta tsaronta, ta yadda kasashen kungiyar za su yi watsi da dogara da Amirka.

A cewar Shugaba Macron bukatar tasa za ta zo baro-baro nan gaba "cikin watanni masu zuwa". Macron ya bayyana haka ne ga jami'an diflomasiya 250 da 'yan majalisa da kwararrun masana tsakanin kasa da kasa da suka hadu bayan dawowa daga hutun bazara.

Wannan bayanan na Shugaba Macron na zuwa ne yayin da kalaman Shugaba Donald Trump ke nunar da yadda shugaban na Amirka ke nuna take-taken nesanta kansa da kungiyar tsaro ta NATO da suke kawance tare ta fiskar samar da tsaro.