1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar binciken amfani da makamai masu guba a Siriya

April 26, 2013

Gwamnatin Amurka ta ce za ta yi kokari wajen ganin Majalisar Dinkin Duniya ta yi bincike game da zargin da ake wa gwamnatin Siriya na yin amfani da makamai masu guba.

https://p.dw.com/p/18O5S
Hoto: Reuters

Kakakin fadar Amurka ta White House Jay Carney ne ya bayyana hakan a wannan Juma'ar inda ya kara da cewar su na da shaidun da ke nuna cewar gwamnatin ta Assad ta yi amfani da makaman masu dauke da guba, baya ga sauran shaidu da a cewarsa sannu a hankali za su bayyana.

A dan tsakanin nan dai tada jijiyar wuya game da wannan zargi da ake wa gwamnatin ta Assad ya yi kamari domin ko a safiyar yau ma sai da Firaministan Burtaniya David Cameron ya bayyana fargabarsa game da wannan batu baya ga kiran da 'yan tawayen na Siriya su ka yi na Majalisar Dinkin Duniya ta sanya baki kan batun ta hanyar gudanar da bincike da kuma daukar mataki cikin gaggawa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu