1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru ta bukaci agajin duniya a yaki da ta'addanci

Muntaqa AhiwaJanuary 13, 2015

Gwamnatin Kamaru ta nemi taimakon sojojin kasa da kasa don yakar barazanar kungiyar Boko Haram, a 'yan kwanakin nan dai mayakan kungiyar sun sha karawa da sojjojin kasar ta Kamaru

https://p.dw.com/p/1EJc9
Kamerun Präsident Paul Biya Archivbild 30.01.2013
Hoto: Patrick Kovarik/AFP/Getty Images

Hakan dai na zuwa ne bayan wani yunkurin da kungiyar ta Boko Haram ta yi a kasar kan sansanin soji, a wannan litinin.

Bukatar tallafin mayakan kasa da kasan dai ta fito ne daga bakin shugaban kasar Kamarun Paul Biya, inda ya ce yanzu barazanar Boko Haram na kokarin wuce makadi da rawa, lamarin da a cewar sa ke bukatar kuzarin kungiyar hada kan kasashen Afirka, dama sauran wasu manyan hukumomi na duniya.

Shugaba Paul Biya ya ma nuna takaicin jan kafa da dakarun kasashen yammacin Afirka ke yi, ga barazanar ta Boko Haram a yankin.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa akalla mayakan kungiyar Boko Haram 143 ne sojojin na Kamaru suka kashe a jiya Litinin, tare da tattara wasu makaman 'yan Boko Haram din. Lamarin ya faru ne a sansanin sojojin Kamaru na Kolofota da ke iyaka da jihar Borno ta Najeriya.

Kamerun Mora Armee Soldaten Anti Boko Haram 07/2014
Hoto: Reinnier Kaze/AFP/Getty Images

Ministan tsaron kasar Edgard Mebe Ngo'o, ya tabbatar da irin ta'asar da sojojin Kamaru suka yi wa ‘ya'yan kungiyar ta Boko Haram din, yana mai cewa Kamaru na fuskantar kungiyar a hari na baya-bayan nan.

"Sojojin mu a yanzu sun fi ko wane lokaci a baya niyyar murkushe ayyukan Boko Haram a kasarsu, musamman arewacin kasar. Suna kuma da cikakken goyon bayan gwamnati da kuma al'ummar kasar. Zan kuma iya tabbatar maku cewa sai mun yi galaba a wannan yaki"

To sai dai akwai wadanda ke ganin fitowar fargaba daga bangaren gwamnatin kasar ta Kamaru duk da kashe mayakan na Boko Haram da dakarun kasar ke yi, da wasu ke ganin wani abu ne da ke iya zama barazana mai girma da kasar ta hango.

Amma fa wani mai nazarin harkokin tsaron yankin yammacin Afirka Mr. Loimeier, ya ce neman agajin da shugaban Kamaru Paul Biya ke yi baya nufin gazawar kasar.

Nigeria Flüchtlinge in Maiduguri
Hoto: picture alliance/AP Photo

"Idan aka duba, lallai yawan sojojin Najeriya ga misali ya fi na Kamaru sosai, don haka neman agaji ga Paul Biya ba zai kasance wani abu ba. Ai ma shugabannin kasashen Afirka sun saba da neman irin agaji haka saboda dalilai daban-daban. Paul biya dai zai iya yin kiran ne, don neman jan hankali wajen ganin yana da niyyar a yaki ta‘addanci da kuma neman makamai na zamani da zasu taimaka a murkushe su"

To yanzu ko ana iya ganin alamun samun wannan agaji ?

Mr. Loimeier, ya ce manyan kasashen waje sun ankara cewar rundunar sojojin Najeriya na sayarwa Boko Haram makamai, kuma kasar Amurka misali, tafi kowa jin takaicin abin da sojin Najeriyar ke yi ganin kayan yaki da suka samar na shiga hannun Boko Haram a karshe. Amma duk da hakan, Amurka da Faransa dama Isra'ila suna da jami'an su na leken asiri a yankin da ake batu a kansa, suna kuma sa ido a kan abubuwan da suke faruwa.

Kungiyar Boko Haram dai na zafafa hare-haren ta ne a kan jami'an tsaro dama fararen hula, ciki harda Musulmi, lamarin da manazarta ke ganin sai an yi tsayuwar gaske kafin a iya shawo kan manufar kungiyar.