1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari zai sake takara

April 9, 2018

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai sake tsayawa takara karo na biyu a babban zaben kasar da za a yi cikin watan Fabrairun badi.

https://p.dw.com/p/2viz2
Muhammadu Buhari speaks during an interview with Reuters at a private residence in Lagos, Nigeria
Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: Reuters/A.Akinleye

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai sake tsayawa takara karo na biyu a babban zaben kasar da za a yi cikin watan Fabrairun badi. Wata sanarwar da ta fito daga ofishin shugaban na Najeriya a yau Litinin ta tabbatar da aniyar shugaba Buhari, abin da ya kwantar da rade-rade na watanni, a ciki da ma wajen kasar.

Da dama daga cikin magoya bayan Buharin dai na cewa babu wani laifin shugaban ya sake takara, yayin kuma da wasu ciki har da tsoffin shugabannin kasar ke ganin shekaru sun ja.

Shugaban dan shekaru 75 a duniya, ya sha jinyar da har yanzu ba a bayyana ta ba a bara, abin kuma  ya kaiga kiraye-kirayen ya ajiye mulkin ya huta. Najeriyar dai na fama da tirkaniyar siyasa da ke ci gaba da raba kan 'yan kasar ta fuskoki da dama.