Buhari ya zauna da majalisar ministoci | Labarai | DW | 30.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari ya zauna da majalisar ministoci

A makon da ya gabata dai Shugaba Buhari ya katse ganawar majalisar ministocinsa da ya saba a ranakun Laraba abin da ya sanya wasu ke ganin shugaban ya koma tsarin nan na ci gaba da aiki daga gida.

Shugaba Muhammadu Buhari a wannan rana ta Laraba ya gana da majalisar ministocinsa a karon farko tun bayan da ya dawo hutun rashin lafiya daga Birtaniya a cikin wannan watan. Shugaba Buhari ya koma Najeriya a ranar 19 ga watan nan na Agusta bayan watanni uku a birnin London inda ya je duba lafiyarsa kan cutar da ba a kai ga fayyace irinta ba.

A makon da ya gabata dai Shugaba Buhari ya katse ganawar majalisar ministocinsa da ya saba a ranakun Laraba abin da ya sanya wasu ke ganin shugaban ya koma tsarin nan na ci gaba da aiki daga gida inda wasu makonnin ya ke halattar taron wasu kuma baya bayyana.

Bayan dawowarsa gida dai shugaban mai shekaru 74 ba a san me ke damunsa ba, kuma wasu jami'ai sun bayyana cewa ya rage tsawon sa'oin da ya kamata ya yi aiki a duk rana.