Buhari ya yi rantsuwar kama aiki | Labarai | DW | 29.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari ya yi rantsuwar kama aiki

A yayin da ake rantsar da shugaban Kasa a Najeriya, Bom ya hallaka mutane bakwai a jahar Borno,a Kaduna matasa sun watsa taron rantsar da gwamna

A tarayyar Najeriya a dazu dazunnan ne aka rantsar da sabon zabebben shugaban kasar Muhammadu Buhari a lokacin wani kasaitaccan biki da aka shirya a yau a babban birnin kasar wato Abuja.Sabon shugaban Kasar ta Najeriya ya bayyana ne a gun wanann biki na rantsar da shi yana mai sanye da manyan tufafi na gari da jampa kana yana rike da littafin Alkur'ani mai tsarki a hannunsa na dama.

Sabon shugaban zai jagorancin milkin kasar ta Najeriya na tsawon wa'adin shekaru hudu inda zai fuskanci manyan kalubale da kasar ta ke fama da su da suka hada da matsalar tsaron da cin hanci da kuma matsalar lantarki dama komabayan tattalin arzikin kasar baki daya.

Sai dai a daidai lokacin da ake bikin rantsar da shugaban kasar, tashin bom ya kashe mutane bakwai a cikin jihar Borno a yayinda wasu matasa suka tarwatsa bikin rantsar da gwamna a Kaduna.