Buhari ya kori shugaban SSS na Najeriya | Labarai | DW | 02.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari ya kori shugaban SSS na Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sallami shugaban hukumar tsaron cikin gida ta SSS Mr Ekpeyong Eta daga bakin aiki tare da maye gurbinsa da Alhaji Lawal Daura.

Shugaba Buhari na Najeriya

Shugaba Buhari na Najeriya

Eta dai na zaman jami'in tsaro na farko da ya rasa mukaminsa a cikin sabuwar gwamnatin ta Tarayyar Najeriya. Wakilinmu na Abuja fadar gwamnatin Najeriya Ubale Musa ya ruwaito cewa ko bayan taka rawa da zargin son zuciya da nuna fifiko yayin yakin neman zabe da akewa hukumar, ana kuma kallon ta da ruwa da tsaki wajen sanya na'urorin leken asiri da za su rinka nuna duk wani abu da sabuwar gwamnatin za ta aiwatar, jim kadan bayan da jam'iyyar PDP ta fadi a babban zaben kasar da ya gudana cikin watan Maris din da ya gabata. Batun saka na'urorin dai ya tilasta gaza tarewar shugaban a fadar gwamnati makwanni kusan uku bayan rantsar da shi.