Buhari ya gargadi Jami′ai masu satar abinci | Labarai | DW | 01.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari ya gargadi Jami'ai masu satar abinci

Gwamnatin Najeriya ta ci alwashin sanya kafar wando daya da masu satar abincin 'yan gudun hijira.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci sufeta janar na 'yan sandan kasar ya kama dukkan jami'an gwamnati da ake zargi da satar abincin da aka yi niyyar kai wa 'yan gudun hijira, wadanda rikicin Boko Haram ya tagayyara a arewa maso gabashin Najeriyar domin zama darasi ga wasu.

A cewar babban mataimaki na musamman ga shugaban Najeriyar kan harkokin sadarwa da kafofin yada labarai malam Garba Shehu, shugaba Buhari ya ce ba zai lamunci halayyar karkatar da taimakon abincin da aka yi niyyar kai wa 'yan gudun hijira ba.

Ya ce babu wani abu na rashin kishi da rashin zuciya ta alheri irin a sace abincin da aka ware wa 'yan gudun hijira.