Buhari ya bukaci hadin kan ′yan Najeriya | Siyasa | DW | 27.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari ya bukaci hadin kan 'yan Najeriya

Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta mika wa shugaban kasar takardar shaidar nasarar zaben mai tasiri wanda, ya yi kira ga hadin kan al'ummar Najeriya.

Kasa da tsawon awoyi da bayana sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarrayar Najeriya, hukumar zaben kasar ta INEC ta mika wa shugaban kasar takardar shaidar nasarar zaben mai tasiri, wajen wani bikin da ya samu halartar jiga-jigai na APC.  Shugaban hukumar zaben Najeriyar mai zaman kanta ta INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya mika wa shugaba  Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo takardun shaidar tabbatar da lashe zaben mai tasiri. Kafin daga baya shugaban kasar ya gudanar da wani jawabin neman hadin kan al’ummar kasar a wani abin da ke zaman yunkurin dinke baraka. A cewar Buhari nasarar da Allah ya bamu ta ishemu biki ba tare da cin zarafin masu adawa ba. Dukkanin 'yan Najeriya daga yau din nan dole su tsaya a matsayi na 'yan uwa domin dora kasa zuwa ga ci gaba da makoma mai kyau.

 

Sauti da bidiyo akan labarin