Buhari ne shugaban Najeriya mai jiran gado | Siyasa | DW | 02.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari ne shugaban Najeriya mai jiran gado

Hakan kuwa ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ƙasar wanda a kansa ɗan takarar jam'iyyar adawa ta APC ya samu gaggarumin rinjaye a gaban abokin hamayyarsa Goodluck Jonathan.

Wannan shi ne karo na huɗu da Janar Muhammadu Buhari yake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya, ba tare da samun nasara ba sai a wannan karon. Ƙasashen duniya dai sun yaba game da yadda zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali, musammun ma dangane da yadda shugaban mai barin gado Goodluck Jonathan ya amince ya sha kaye a zaɓen.Mun tanadar muku rahotanni daban-daban da ma sharhi na musammun a kan batun.

DW.COM