Jonathan ya amince da shan kaye | Labarai | DW | 31.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jonathan ya amince da shan kaye

Dan takarar jam'iyyar PDP da ke mulki ya yarda cewa ya sha kaye a zaben shugaban kasa a Najeriya. Amma har yanzu INEC ba ta bayar da cikakken sakamakon zaben ba.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gana da babban madugun adawa Janar Muhammadu Buhari ta wayar tarho a yau Talata inda ya mika wuya bisa kayen da ya sha a hannunsa a zaben kasar da aka yi da jam'iyyar APC ta samu rinjaye.

A tattaunawar da aka yi da misalin karfe hudu da minti hamsin da biyar shugaba Jonathan ya taya Muhammadu Buhari murna kamar yadda Lai Mohammed da ke magana da yawun jam'iyyar ta APC ya bayyana.

Har yanzu dai babu sakamakon da ya fita daga hukumar ta INEC kan wannan nasara ta APC a hukumance amma sakamakon da ake kirgawa ya zuwa yanzu, ya nunar da cewa Muhammad Buhari ya ba wa shugaba Jonathan ratar gaske a sakamakon abinda ya sanya dubun dubatar al'umma a wasu sassan kasar ta Najeriya suka fita dan yin murna.