1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habaka dangantaka tsakanin Abuja da Pretoria

Zainab Mohammed Abubakar
October 3, 2019

Shugaban Najeriya da ke ziyara a Afirka ta Kudu da takwaransa Cyril Ramaphosa sun kaddamar da tattaunawar hadin gwiwa a birnin Pretoria da nufin karfafa dangantakarsu ta kasuwanci.

https://p.dw.com/p/3Qh0H
Südafrika Muhammadu Buhari und Cyril Ramaphosa
Hoto: Reuters/S. Sibeko

Ziyarar ta kwanaki uku ta shugaba Buharin, za ta mayar da hankali ne wajen karfafa dangantakar kasuwanci da hadin kai tsakanin  kasashen biyu.

Sai dai wannan yunkurin na zuwa ne a lokacin da dangantakar kasashen biyu ke cikin tangarda , biyo rikicin kyamar baki da ya tilasta daruruwan 'yan Najeriya koma kasarsu ta asali.

A taron manema labaru na hadin gwiwa, shugabannin kasashen afirkan biyu sun jinjinawa yadda lamura ke tafiya.

Sai dai dukkanninsu biyu sun tabo rikicin kyamar bakin, rikicin da ya tilasta Najeriyar aikawa da jakada na musamman domin bayyana kokenta kan harin da ake kaiwa 'yan kasar da ke zaune a Afirka ta Kudun da ma wuraren kasuwancinsu. Inda daga bisani ita ma Afirka ta Kudun ta aike da nata jakada domin neman afuwar Najeriyar.