Buhari da Atiku mai rabo ka dauka a APC | Siyasa | DW | 10.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Buhari da Atiku mai rabo ka dauka a APC

Wannan zaben fidda gwani dai na zama wata manuniya kan irin rawar da jam'iyyar mai adawa za ta taka a zaben da ke tafe a shekara mai zuwa a Najeriyar.

A ranar Larabannan da Bahause ke kira “ta bawa ranar samu” (10.12.2014) ta kasance rana da ake zaben fidda gwani a babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wato APC dan tunkarar jam'yya mai mulki ta PDP wacce ita ma ke nata taron dan jadda wa shugaban Jonathan takararsa a zaben na shekara ta 2015.

A filin wasan na Teslim Balogun da ke jihar Legas kudu maso yammacin Najeriya ‘yan takara da ke gaba-gaba Janar Mohammadu Buhari mai ritaya da Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya lokacin mulkin Obasanjo.

Ita kuwa a nata bangaren jam'iyya mai mulki PDP a taron nata na Abuja fadar gwamnatin Najeriya jaddawa kawai za ta yi shugaba Jonathan ya yi mata takara a zaben na badi.

Fiye da wakilai 8,000 ne dai ake sa ran zasu kada kuri'a a wannan zaben na fidda gwani na Jam'iyyar ta APC.

Sauti da bidiyo akan labarin