1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Buhari ya nemi allurar riga-kafin corona

Ramatu Garba Baba
September 23, 2020

Shugaba Buhari na Najeriya ya nemi MDD da ta dauki mataki guda don ganin an wadata kowacce kasa da allurar riga-kafin cutar Corona a sabanin yadda wasu kasashe masu karfin tattalin arziki ke nema wa kansu kadai mafita.

https://p.dw.com/p/3irwj
UN-Generalversammlung in New York | Muhammadu Buhari, Präsident Nigeria
Hoto: Reuters/L. Jackson

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nemi a samar da ingantacciyar allurar riga-kafin cutar Coronavirus ga dukkan jama'a ba tare da nuna son kai ba. Shugaban dai ya nemi Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakin shawo kan annobar, ya ce kin yin hakan zai nuna gazawarta a cika muradun da aka gina majalisar a kai.

Kalaman Shugaban na Najeriya, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin, kasashen duniya masu karfin tattalin arziki ke samarwa kansu mafita ta hanyar kulla yarjejeniya da manyan kamfanonin sarrafa magunguna don wadata su da isassun allurar riga-kafin cutar ba tare da yin la'akari da kasashe matalauta ba. 

Batun annobar Coronavirus da ta bulla a kasar Chaina a Disambar bara, ce dai ta mamaye babban taron Majalisar Dinkin Duniya na bana. Covid-19 ta janyo asarar rayuka kusan miliyan daya baya ga wasu sama da miliyan talatin da ta kama a sassan duniya.