Bude filin jirgi a Hong Kong bayan lafawar zanga-zanga | Labarai | DW | 14.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bude filin jirgi a Hong Kong bayan lafawar zanga-zanga

Duk da yake wasu daga cikin masu zanga-zangar sun kwan a filin jirgin, an sake bude jigilar matafiya a filin jiragen saman Hong Kong da aka rufe a ranar Talata sakamkon zanga-zanga.

An sake bude filin jirgin sama a HongKong da sanyin safiyar wannan Laraba sa'o'i bayan dakatar tashin jiragen sama a filin jirgin bisa kazancewar zanga-zangar neman sauyi a Hong Kong da ta bazu zuwa harabar filin.

Sai dai sake buda filin jirgin na zuwa a daidai lokacin da kasar China ta zargi cin zarafin 'yan kasarta biyu a yankin na Hong Kong, sakamakon likida masu kashi da masu zanga-zangar suka yi, lamarin da kuma kasar ta kira da ta'addanci.