British Airways zai cigaba da zuwa Masar | Labarai | DW | 26.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

British Airways zai cigaba da zuwa Masar

Kamfanin jiragen sama na British Airways zai koma jigilar matafiya kasar Masar a ranar wannan Juma'ar biyo bayan dakatar da sufuri har na tsawon mako guda bisa dalilan tsaro.

Yayin da kamfanin ke sanar cigaba da komawa jigilarsa a kasar ta Masar, ya ce tsaron lafiyar fasinjoji da ta ma'aikatan jiragen shi ne babban abin da ya sanya a gaba.

A ranar Asabar din da ta gabata ce kamfanin ya sanar da jingine dauka da sauke fasinja a babban birnin kasar ta Masar duk kuwa da cewar kawo yanzu masu ruwa da tsaki a kamfanin basu bayyana dalilan tsaron da suka haifar da wannan takaitaccen tsaiko ba, shima kamfanin jiragen sama na Lufthansa mallkar kasar Jamus ya dakatar da zuwa babban birnin na Masar amma na kwana guda, al'amarin da mahukuntan kasar Masar suka soka da kakkakusar murya.