1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amazon: Matsin lamba kan shugaban Brazil

Zulaiha Abubakar
August 29, 2019

Shugaba Jair Bolsonaro na kasar Brazil ya aikawa kasashen Kudancin Amirka takardar gayyata don nemo hanyoyin ciyar da dajin Amazon gaba da kuma kare shi daga gobara.

https://p.dw.com/p/3Ohgu
Brasilien Waldbrände
Hoto: picture-alliance/AP/E. Peres

Matakin na zuwa ne bayan da shugaban ya zargi kasashen Jamus da Faransa da yunkurin ruguza Brazil a matsayin dunkulalliyar kasa ta hanyar amfani da kudin tallafin kashe gobarar a lokacin taron kasashe masu karfi tattalin arziki wato G7.

Ko da yake shugaban kasar ta Brazil ya bayyana cewar zai iya amincewa da kudaden agajin amma sai shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya janje wasu kalamai da yayi kan batun gobarar dajin na Amazon, indaministan harkokin kasashen wajen Brazil Ernesto Araujo ya bayyana cewar gwamnatinsu na takaicin yadda Macron din ke daukar kansa tamkar wanda ya fi kowa damuwa da al'muran da suka shafi muhalli.
 


.