1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brazil na fama da masifar ambaliya

January 13, 2011

Mutane kimanin 335 sun rasa rayukansu a ambaliyar ruwa Brazil yayin da aikin ceto ya kankama

https://p.dw.com/p/zx7m
Ana cikin mummunan yanayin muhalli a BrazilHoto: AP

Masu aikin agajin gaugawa a ƙasar Brazil na can na ta ƙoƙarin gudanar da aikin ceto domin zaƙulo mutane da laka ta danne a sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka ɗauki tsawon sa'o'i 24 ana yi, wanda aka daidaita yawansu da ruwan sama na wata guda da aka shattata akan yankunan dake kan tsaunika dake kudu maso yammacin ƙasar, wanda suka haddasa mummunar ambaliya tare da zabtarewar ƙasa.

Masu aiko da rahotanni sun ce mutane da dama suna cikin barci ambaliyar ruwan ta rutsa da su. Mutane aƙalla 335 suka rasa rayukansu,a garin Tresopoli dake da ratar kilomita 100 daga Rio de Janeiro, inda mutane 130 suka mutu yayin da wasu 107 suka cika a garin Nova kana wasu 13 a Sao Paulo. Wani jami'in gwamnati a yankin ya ce ba mamaki yawan mutane da abin ya shafa su ƙaru nan gaba domin kuwa ya ce har yanzu akwai ƙauyukan da masu aikin agajin ba su kai garesu ba.

Yanzu haka dai gwamnati ta aike da jirage masu saukar angulu domin ceton jama'ar.

Luiz Fernando Pez shine mataimakin gwamnan Rio de Janeiro.

"Mun tura motoci da jiragen sama suna ta gudanar da aikin ceton kuma muna sa ran za a samu wasu jama'ar da rai.

Mawallafi: Abdurrahmane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal