1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bouteflika: Ba zan kammala wa'adi ba

March 4, 2019

Shugaban kasar Aljeriya, ya yi wasu kalamai kan wa'adin mulkin kasar da zai fafata a watan gobe na Afrilu, kalaman kuma na neman alfarmar 'yan kasar da ke zanga-zanga a yanzu.

https://p.dw.com/p/3EOf2
Algerischer Präsident Abdelaziz Bouteflika
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kramdi

Shugaba Abdelaziz Bouteflika na kasar Aljeriya, ya yi alkawarin cewar ba zai kammala wa'adin da yake nema na shugabancin kasa ba, idan har aka sake ba shi damar mulki a zaben watan gobe na Afrilu da za a yi a kasar.

Shugaban dai na wadannan kalamai ne, yayin da zanga-zanga ke kara zafi daga masu adawa da ci gaba da mulki da yake yi da a yanzu ya doshi shekaru 20.

A shekara ta 2013 ne dai Shugaba Bouteflika, ya kamu da cutar shayewar wani sashe na jiki.

Daruruwan dalibai ma dai sun yi dafifi a Algiers da wasu manyan biranen kasar a jiya, duk a adawa da mulkin shugaban mai shekaru 82. 'Yan sanda sun yi ta fesa ruwan zafi kan masu boren, a kokarin hana su isa muhimman wurare a birnin na Algiers.