Bore kan wutar daji a Brazil | Labarai | DW | 23.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bore kan wutar daji a Brazil

Fiye da mutun 200 ne suka yi gangami a gaban ofishin jakadancin kasar Brazil da ke birnin Landan a yunkuri na ganin hukumomi sun yi wani abu don murkushe gobarar daji Amazonie da ke cigaba da barna a Brazil.

Dauke da allunan da ke kunshe da sakonni masu cewa ku ceci duniyarmu, masu zanga-zangar sun yita furta kalaman nuna rashin jin dadi da irin barnar da wutar dajin ke ci gaba da haifar wa Brazil.

Wannan zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gba da matsin lamba ga shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro da ya gagauta daukar matakai game da gorara dajin.

Suma dai kungiyoyin matasa yan makaranta masu fafatukar kare muhalli na "Fridays for Future" sun kara sanya batun gobarar dajin ta Brazil a cikin jerin gangamin da suke gudanarwa a ko wace ranarkun Juma'a musamman a biranen Berlin, Madrid, Barcelona, da Turen da ke Arewacin Italiya.