Boko Haram ta saki sabon sako | Labarai | DW | 13.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta saki sabon sako

Kungiyar mayakan Boko Haram ta saki wasu sabbin faya-fayen bidiyon da ta nuno wasu da ke ikirarin 'yan matan makarantar Chibok ne da suka ki a cetosu a musayar da gwamnatin Najeriya ta yi da 'yan kungiyar kwanakin nan.

Cikin bidiyon mai tsawon minti shida, wata Maida Yakubu da ke rike da bindiga tare da wasu 'yan matan uku cikin lullubi, ta bayyana mubaya'arta ga kungiyar.

A cewar yarinyar ba zata koma gida ba, saboda iyayenta na zama a garin kafirci, abin kawai da take so shi ne su musulunta, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya labarta.

Haka zalika, wasu kwamandojin kungiyar cikin damara irin ta soji, da suka yi ikirarin su ne gwamnatin Najeriya ta yi musayar da su, sun ce za su ci gaba da kai hare-hare a Abuja fadar gwamnati da ma wasu manyan garuruwan Najeriya.   

A makon da ya gabata ne dai 'yan matan makarantar Chibok 82 daga cikin wadanda kungiyar ke garkuwa da su shekaru uku, suka fito bayan tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar.