1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta sace wasu mutane a Kamaru

Mouhamadou Awal BalarabeJanuary 18, 2015

'Yan bindigan Kungiyar Boko Haram sun yi kashe-kashe da sace-sacen mutane a arewacin kasar kamaru lokacin da suka Kai hari.

https://p.dw.com/p/1EMOr
Hoto: picture alliance/AP Photo

Kungiyar da aka fi sani da suna Boko Haram ta sake kai wani sabon hari a arewacin kasar kamaru, inda ta kashe mutane da dama tare da sace wasu akalla 60. Majiyar 'yan sanda da ta bayar da wannan sanarwa ta ce akasarin wadanda harin ya shafa mata ne da kuma kananan yara. sai dai kuma ba ta bayar da adadin mutanen da harin ya ritsa da su ba.

Da sanyin safiyar wannan rana ta Lahadi ne dai 'yan bindigan na Boko haram suka kutsa wasu kauyuka biyu dake karamar hukumar Mokolo a yankin kuri'ar arewacin Kamaru domin aikata ta'asa. Hare-hare sun zama ruwan dare a wannan yanki tun bayan da gwamnatin Kamaru ta sha alwashin sa kafar wando guda da 'yan Boko Haram, sakamakon barazanar da suke yi ga zaman lafiya a kasashen dake magwabtaka da tarayyar Najeriya.

Kasar ta kamaru ta jibge sojoji da kuma makamai a kan iyakarta da arewacin tarayyar Najeriya domin kare kanta daga hare-haren wannan kungiya dake gagwarmaya da makamai. Sai dai kuma ta nemi kasashen duniya su kawo mata dauki domin ta samu murkushe wnanan kungiya. Tuni dai kasar Chadi ta amsa wannan kira inda ta tura da kayan yaki da kuma sojojin domin mara wa kasar ta Kamaru baya.