1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta kashe jami'ar agaji

September 17, 2018

Mayakan Boko Haram a Najeriya sun kashe wata ma'aikaciyar jin kai da suka sace a watan Maris a garin Rann na jihar Borno.

https://p.dw.com/p/352cG
Boko Haram
Hoto: Java

Rahotannin da ke fitowa daga yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na cewa mayakan Boko Haram sun hallaka daya daga cikin mata ma'aikatan jin kai da suka sace a watan Maris a garin Rann shelkwatar karamar hukumar Kala-Balge a jihar Borno.

Ofishin da ke kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Dunya ya tabbatar da kisan da mayakan na Boko Haram suka yi wa Saihura Hussaini Ahmed, da ke aikin unguwarzoma.

A ranar daya ga watan Maris na wannan shekarar ne wasu mayakan Boko Haram suka kai hari garin Rann inda suka yi awon gaba da mata jami'an kiwon lafiya su uku.

Ana dai bayyana fargaba kan kada mayakan su kai ga halaka sauran wadanda suke ci gaba da garkuwa da su.