Boko Haram ta halaka mutane 32 a Kamaru | Labarai | DW | 26.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta halaka mutane 32 a Kamaru

Hukumomin kasar Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane 32 a yayin da wasu 86 suka ji rauni a cikin hare-haren kunar bakin wake da Kungiyar Boko Haram ta kai a kauyen Bodo na Arewa mai nisa

A kasar Kamaru alkalumman baya-bayan nan wadanda hukumomin kasar suka bayyana sun nunar da cewa mutane 32 ne suka halaka a yayin da wasu 86 suka ji rauni a cikin tagwayen hare-haren kunar bakin wake da Kungiyar Boko Haram ta kai a jiya Litinin a saman kasuwar kauyen Bodo na Arewa mai nisa kusa da kan iyakar kasar da Najeriya.

Gwamnan yankin Arewa mai nisa na kasar ta Kamaru Midjiyawa Bakari ya bayyana wannan hari wanda ya ce wasu kananan 'yan mata ne 'yan kunar bakin wake suka kai shi a matsayin mafi muni da yankin ya taba fiskanta tun bayan da Boko Haram ta soma kaddamar da hare-harenta a kasar ta Kamaru a shekara ta 2013.

Tun daga wancan lokacin dai Kungiyar ta Boko Haram ta kaddamar da hare-hare sama da 30 a kasar ta Kamaru, da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane dudu da 200 da suka hada da sojojin gwamnati 67 da 'yan sanda uku.