Boko Haram sun hallaka soja da farar hula a Nijer | Labarai | DW | 28.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram sun hallaka soja da farar hula a Nijer

Harin da aka kai shi cikin dare a farkon makon nan ya faru ne a garin Abadam na yankin Diffa da ke iyaka da Najeriya.

Nigeria Soldaten in Diffa Aktion gegen Boko Haram

Soja kan aiki a yankin Diffa

Wasu mahara da a ke zargin mayakan Boko Haram ne sun kaddamar da hare-hare a wani kauye da ke a kudancin Niger, harin da yayi sanadin kisan mutane uku ciki kuwa har da soja a cewar majiyar jami'an tsaro a jiya Alhamis.

Harin da aka kai shi cikin dare a farkon makon nan ya faru ne a garin Abadam na yankin Diffa da ke iyaka da Najeriya.

A cewar wata majiya ta sojin Nijer harin da mayakan suka kai a daren ranar Talata ya yi sanadin kisan mutane biyu fararen hula sannan wani soja daya mai mukamin saja ya halaka a lokacin da dakarun sojan na Nijer ke fatattakar mayakan.

Wata majiyar ma ta tababbar wa 'yan jarida faruwar harin bisa sharudan ba za a bayyana sunansu ba.