Boko Haram sun hallaka dalibai a Yobe | Labarai | DW | 29.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram sun hallaka dalibai a Yobe

Dalibai fiye da 40 sun hallaka a wata makanta da ke Jihar Yobe a yankin Arewa maso Gabashin taryyar Najeriya bayan da 'yan bindiga suka kai hari.

Yawan mutanen da suka mutu sun kai 42 sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai wata makaranta da ke Jihar Yobe a yankin Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya. Da sanyin safiyar wannan Lahadin ne maharan suka far wa daliban lokacin da suke barci kamar yadda kwamishinan 'yan sandan jihar Sanusi Rufai ya tabbatar wa Reuters. Rahotanni daga kamfanonin dillancin labarai daban daban sun ce an kai harin a kwalejin koyon aikin gona da ke garin Gujba a Jihar ta Yobe.

Wani kakakin jami'an tsaro ya daura alhakin harin kan kungiyar Boko Haram wadda ta yi kaurin suna wajen kai hare-hare a cikin yankin. Ana daura wa kungiyar alhakin hare-hare na baya da aka kai a kan makarantu. A watan Mayu ne gwamnatin Tarayyar ta Najeriya ta kafa dokar ta baci a wasu jihohi uku, domin dakile rashin tsaro da ya yi katutu a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe