Amirka za ta taimaka wa Turkiyya
February 19, 2023
A wannan Lahadin Sakataren Harkokin wajen Amirka Antony Blinken ke kai ziyara kasar Turkiyya don ganewa idanunsa girman ta'asar da iftla'in da girgizar kasa ta haifar a yankin kudancin kasar. Ana sa ran babban jami'in zai gana da Shugaba Recep Tayyip Erdogan don tattauna batutuwa da suka shafi taimakon da kasar ke bukata a yanayin da ta tsinci kai.
A ranar shida ga wannan watan na Fabrairu, girgizar kasa mai karfin maki 7.8 a ma'aunin Rista, ta auku a yankin kudancin Turkiyya da arewacin Siriya, kawo yanzu mutum fiye da dubu arba'in da biyar aka tabbatar sun mutu a yayin da wasu fiye da miliyan daya suka rasa matsuguninsu baya ga dubban da ke jinya a asibiti. Masana tattalin arziki na hasashen cewa, kasashen na bukatar biliyoyin dalloli kafin su sake iya gina yankunan da iftala'in ya lalata.