1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 40 da murabus din Ahidjo na Kamaru

Zainab Mohammed Abubakar
November 4, 2022

Kwanaki biyu kafin bikin cika shekaru 40 na mulkin Paul Biya a Kamaru, a yau ne shugaban kasar na farko Ahmadou Ahidjo ya cika shekaru 40 da yin murabus bisa dalilai na lafiya.

https://p.dw.com/p/4J4rF
Paul Biya Präsident Kamerun
Hoto: AP

Shi dai Biya mai shekaru 89 da haihuwa ya zama daya daga cikin shugabanni mafi dadewa a mulki a duniya, godiya ga mukarrabansa da ke rike da manyan mukamai.

Bayan shekaru bakwai na zama firaminista, Biya ya hau karagar mulki a ranar shida ga Nuwamban 1982, inda ya kasance shugaban kasa na biyu tun bayan da Kamaru ta samu 'yancin kai a 1960.

Rigingimun siyasa da zamantakewa ta rashin tsaro na daga cikin matsalolin da suka dabaibaye tsarin mulkinsa na sai madi-ka-ture, daura da matsaloli na tattalin arziki.

Tun bayan faduwar Robert Mugabe a shekarar 2017, Biya ya zama shugaban Afrika mafi tsufa kuma na byu mafi dadewa a kan mulki bayan na Equitorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo.