Birtaniya za ta karawa Najeriya kudaden agaji | Labarai | DW | 31.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya za ta karawa Najeriya kudaden agaji

Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson, ya ce Birtaniya za ta samarwa yankin arewa maso gabashin Najeriya da kudi dalar Amirka 250 da nufin inganta yankunan da rikicin Boko Haram ya yi wa illa sosai.

Münchner Sicherheitskonferenz (REuters/M. Dalder)

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Boris Johnson.

Itama ana ta banagaren sakatariyar raya kasashe ta Birtaniya Priti Patel, da take bayyana aniyar kasar a kan kudaden agajin a yayin da suka ziyarci yankunan da ta'addancin Boko Haram din ya shafa a jihohin da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta ce za'a raba Kudaden tallafin ne a cikin shekaru hudu nan gaba.

A yanzu dai sama da mutane miliyan guda ne ke fuskantar barazanar yunwa a Najeriya sakamakon rashin tasirin noma, amma suna da yakinin wadannan tallafi ka iya farfado da harkokin more rayuwa da zai ingata fannin kiwo lafiya da Ialimi.