Binciken take hakkin dan Adam a Gaza | Labarai | DW | 12.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken take hakkin dan Adam a Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan batun take hakkin dan Adam da ake zargin Isra'ila ta aikata a yankin Zirin Gaza.

Tun bayan da kasar ta Isra'ila ta kaddamar da kai hare-hare a yanki Zirin Gaza cikin watan Yulin da ya gabata, kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke nuna yatsa ga kasar dangane da yadda take kai hari a kan fararen hula musamman ma mata da kananan yara. Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya dai ta zargi Isra'ilan da kuma kungiyar Hamas da take hakkin dan Adam a fafatawar da suke a tsakaninsu. Kwamitin binciken dai na karkashin jagorancin wani kwararren lauya dan asalin kasar Kanada Farfesa William Schabas yayin da kwararren masanin hakkin dan Adam dan kasar Senigal Doudou Diene da kuma wata lauya 'yar asalin kasashen Birtaniya da Lebanon Amal Alamuddin za su kasance mambobin kwamitin. Kawo yanzu dai bangarorin biyu na ci gaba da tattaunawa a kasar Masar domin lalubo bakin zaren warware rikicin da ke tsakaninsu.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu