Binciken kashe-kashen sabuwar shekara a Rivers | Siyasa | DW | 02.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Binciken kashe-kashen sabuwar shekara a Rivers

Wasu rahotanni na ganin cewa mutane 35 ne aka kashe a lokacin da 'yan bindigar suka bude wuta ga masu bikin ranar sabuwar shekara a jihar Rivers da ke Kudancin Najeriya.

Rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta bayyana cewar ta fara samun bayanai da za su kai ga kamo wasu 'yan bundiga da suka bude wuta kan dandanzon wasu masu bikin Kirsimeti da kuma shiga sabuwar shekarar da muke ciki ta 2018 a garin Omoku da ke jihar Rivers, inda kuma aka nunar mutane kimanin 35 sun hallaka, cikinsu kuwa har da mata da kananan yara.

Wani Mista Magnus Okorogba da ke zaman dan asalin garin na Omoku da a kai wannan kashe-kashe, ya ce mutanen na kan murnar fatan shiga sabuwar shekara ta 2018, kuma suna tsaka da annashuwa da harba wutar "KnockOut" kawai sai ga wasu 'yan bundiga sun bayyana, suka bude musu wuta kan mai uwa da wabi, da ma dai tashin hankali a wannan gari ba sabo ba ne, sai dai an dan samu kwanciyar hankali.

Yayin da wadanda suka ganewa Idanuwansu ke fadin mutane 30, wasu kuma na cewar 35 ne, su kuwa hukumomi na kafewar cewa mutane 16 kawai suka mutu, sai kuma wadanda suka jikkata.

Nigeria Delta Polizei PK (DW/M. Bello)

Nnamdi Omoni me magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Rivers

Nnamdi Omoni, shi ne mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar ta Rivers, ya yi karin haske kan halin da ake ciki:

"Wadanda aka jikkata din mun kai su asibiti, kuma jimuwar da suka yi ba mai tada hankali ba ce, sannan labari mai dadi shi ne cewar masu jikkatar na murmurewa, sannan kuma tuni an dawo da doka da oda a wannan gari, jami'an tsaro tuni suna garin don aikin tsaro na musamman, kuma muna sane da cewar wannan gari na Omok gari na 'yan tada hankali ne, amma mun shawo kan lamarin watanni shida baya, sai dai kuma 'yan tada hankulan sun shammace mu, amma ina tabbatar da cewar muna nan muna bin sawun wadannan 'yan bindiga, kuma tuni ma muka samu sahihan bayanai da babu haufi kamar ma mun kamasu."

Za a iya cewar, garin na Omoku da ke karamar hukumar Onelga na jihar Rivers da wannan kashe-kashen sabuwar shekara ya faru, da ma kananan hukumomin Ahoada ta  gabas da kuma ta Yamma, duka makwabta juna a Jahar ta Rivers ,da ke yankin Niger Delta, sun dau kimani shekaru kusan bakwai cikin rikicin al'ummomi da 'yan kungiyoyin asiri da ake zargin 'yan siyasa na assasawa.

Sauti da bidiyo akan labarin