1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bincike ya nuna cewa talauci ya ƙaru a Najeriya

November 13, 2013

Duk da iƙirarin cigaban da Najeriya ke yi na samun cigaba, Bankin Duniya ya ce kusan milliyan ɗari na 'yan ƙasa na rayuwa cikin talauci

https://p.dw.com/p/1AHBJ
©James Keogh/Wostok Press/Maxppp Nigeria, Lagos 29/11/2012 The city of Lagos counts more than 15 millions en people and has to deal with more than 200 000 new arrivants every year. 70% of its population lives inside a slum like Makoko build in some part on the lagoon.
Hoto: picture alliance / dpa

A wani abun dake zaman alamu na baya ba zane ga Tarrayar Najeriyar dake iƙirari na cigaba, Bankin Duniya ya ce 'yan kasar kusan miliyan 100 ne ke rayuwa irin ta babi ya Allah duk da iƙirarin gwamnatin ƙasar na kusan isa tudun mun tsira.

A cikin ƙanƙanen lokaci ne dai suka kai ga fintikau ga masu arziƙi a ɗaukacin nahiyar Afirka, haka kuma yanzu suna tabbatar da sabon tarihi na yawan fatara a cikin nahiyar ga tarrayar Najeriya da Bankin Duniya ya ce ta na taƙama da masu rayuwar almajirci miliyan sama da 100 a cikin ta.

Duk da iƙirari na ƙaruwar arziƙin da babu kamar ta cikin 'yan shekarun nan dai wani rahoton Bankin na Duniya dai ya ce aƙalla kaso 8 cikin dari na ɗaukacin rayuwa irin ta almajirci a duniya baki ɗaya dai na faruwa ne tsakanin al'ummar ƙasar dake taƙama da arziƙin man fetur amma kuma rayuwarsu ke daɗa baya kusan kullum.

slums in lagos, Nigeria
Wata unguwar talakawa a LegasHoto: picture-alliance / Ton Koene

Baƙatun Najeriya bisa bayyanan Bankin Duniya

Babbar jami'ar bankin dake tarrayar Najeriyar Merie Francoise Marie Nelly dai ta ce ƙasar na buƙatar namijin ƙoƙari kafin iya rabuwa da talaucin da ya yi katutu a cikin rayuka na al'ummar ƙasar, sannan kuma ke neman wucewa da sannin mahukuntan ta.

Tuni dai dama ƙasar ta ce ta sallama ga burin rage talauci na burikan ƙarnin dake shirin cika cikin wasu shekaru biyu masu zuwa, duk da dubban miliyoyin da gwamnatoci a matakai daban-daban ke rabuwa dasu da sunan babban yakin na talauci.

To sai dai kuma a faɗar Dr Jibo Ibrahim dake jagorantar cibiyar tabbatar da demokaradiya da cigaba mai zaman kanta cikin tarrayar Najeriya rahoton da bankin ya fitar dai na zaman tabbacin dake nunin cewar tuni fa mahukuntan ƙasar suka kauce daga hanyar da suke iƙirarin ta kusan kai 'yan ƙasar tudun mun tsira.

Yunƙurin da ƙasa ta yi a baya

Kama daga sabon shirin gwamanatin kasar na Sure-P ya zuwa ga hukumar yaƙi da batun fatara ta cikin ƙasar dai an ɗauki matakai daban-daban da ma dabaru na tunanin kafa tarihin ceto 'yan kasar daga arziƙi na ruwan da ya gagare su sha duk da kishirwa.

To sai dai kuma gizon ƙasar ta Najeriya na saƙar ne tare da mai da irin waɗannan shirye shiryen ya zuwa kafa ta sakaya wa siyasa maimakon taimakawa yaƙi da talauci a zahiri a faɗar Ahmed Babba Kaita dake zaman wani ɗan majalisar wakilan ƙasar da ta daɗe tana kasafi da nufin yaƙi da talaucin amma kuma ta daɗe tana kallon talaucin yana ƙara ƙaruwa a birane da ƙauyuka.

Ya zuwa ranar yau dai ƙasar ta Najeriya ta ce tana taƙama da kusan dalar Amirka miliyan dubu 44 cikin asusun ajiyar ta dake waje kudaden kuma dake zaman akalla Naira dubu 72,000 da ke iya zaman jarin fara sana'a ga kusan dukkannin miliyoyi 100 na yan kasar da bankin na duniya yace suna babu ya Allah.

In this image taken Thursday Feb. 28, 2013 people search for goods through the rumbles of a demolished houses at Ijora Badia slum in Lagos, Nigeria. The bulldozers arrived at dawn to this neighborhood of shanty homes and concrete buildings in Nigeria’s largest city, followed by police officers in riot gear carrying Kalashnikov assault rifles. The police banged on doors, corralling the thousands who live in Ijora-Badia off to the side as the bulldozers’ blades tore through scrap-lumber walls, its track grinding the possessions inside into the black murk of swamp beneath it. It left behind only a field of debris that children days later picked through, their small hands dodging exposed rusty nails to pull away anything of value left behind. (AP Photo/Sunday Alamba)
Masu roro bayan an rusa gidajeHoto: picture alliance/AP Images

To sai dai kuma a fadar Dr yarima lawal Ngama dake zaman ƙaramin ministan kuɗin ƙasar ta Najeriya dai wai ba daga nan ne gwamnatin take kallon mafita a cikin matsalar ba.

Zaman jiran gani a ƙasa dai wai na zaman karatun kare da yan bikin dake sharholiya cikin gidan su.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Saleh Umar Saleh