1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bin kadin yunkurin kafa kamfanin jiragen saman Najeriya

Uwais Abubakar Idris AMA
November 6, 2020

A Najeriya kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa sun fara bin bahasin makudan kudadden da ake warewa don yunkurin kafa kamfanin jiragen saman Najeriya mallakar gwamnati.

https://p.dw.com/p/3kxZb
Nigeria Kaduna International Airport Flughafen
Hoto: Getty Images/AFP

Tsabar kud Naira bilyan 14.1 ne aka ware cikin shekaru uku don samar da sabon kamfanin jirgen sama a Najeriya matsayin yunkurin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka na samar da kamfanin sufurin jieragen saman na kanta mai suna Nigeria Air, tare da ware Naira bilyan 8.5 a shekarar 2019, haka a shekarar 2020 aka ware Naira bilyan 4.6, da kuma tanadin Naira bilyan guda shekara mai zuwa, sai dai har yanzu ko kamshin kamfanin sufurin jiragen saman na Air Nigeria ba a ji.

Karin Bayani: Sabon kasafin kudi don ci gaban tattalin arzikin Najeriya

Tun bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari kan karagar mulki a shekarar 2018 zuwa yanzu haka bata cimma ba a yunkurin Najeriyar na samun kamfanin sufurin jiragen sama mallakar gwamnati. Wannan lamari ya sa jama'a da dama tambayar abin da ke faruwa bayan da aka sanya tsarin a cikin kasafin kudi amma kuma a ji shiru. Rashin samun kamfanin sufurin jiragen sama malakarar Najeriya na zama abin kunya ga kasar mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka a daidai lokacin da ake zargin da akwai cin hanci a wannan fanin. 

Karin Bayani: Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin 2020

Daga jiragen sama 30 da tsohon kamfanin Nigeria Airways ya mallaka a shekaru 20 da suka gabata har suka dawo zuwa uku kacal kafin durkusar da kamfanin. Za'a sa ido a ga ko gwamnatin za ta cika alkawarin da ta dauka inda ministan sufurin jiragen saman Hadi Sirika ya kara jadadda cewa lallai za su samawa kasar kamfanin sufurin jiragen sama na kanta kafin karshen wa'adin mulkin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a 2023.